WELLCOME TO JAFAR GIGINYU

wannan wata damace ta mai rabo saboda samun gara basa a wannan waje mai tarin farin jini

Sunday, January 22, 2006

TARIHINA

ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMTULLATARIHI
JAFAR MOHD GIGINYU
Anhaife a unguwar giginyu ranar (11-12-1984).nayi makarantar primary dake giginyu wato Giginyu special primary School daganan na tafi makarantar gabada primary wato Stadium Goverment secondary school nafar a(1996-2001)daganan na koma goverment secondary school mariri kano inda na karasa.sannan na halarci makarantu masu zaman kansu wato makrantun na ura mai kwakwalwa kamar Gem computer Academy /SasilNET Cafe nayi karatun allo a makaranta daban daban akwai makarantar malam lawan wato Miftahul Ibadat Islamiyya giginyu,bukhari islamiyya giginyu,Deenwattahazif islamiyya giginyu, sannan akwai makarantun allo kamar haka,makarantar malam Ayuba ,makarantar malam Amadu.AIKINafara aiki shekarata dubu biyu a kamfanin hada lemo watoBaffas Nig Ltd,sannan natafi kamfanin kimiyya na yanar gizo wato Megatech Network.

KUNGIYOYI
Nafara da kungiyar wasan kwaikwayo ta Danmowa Drama Group /Ruwandare Drama Group Giginyu Drama & Salsan Production /Galaxy film Production Garkuwa Drama Clubsannan na halarci kungiyarnanta Nigeria Boys Scout/nakuma halarci wasu kungiyoyi kamar Ahip/Yehdi,sansan na kasance acikin kungiyoyi na siyasa daban daban ------------------------------------------------------------------------------------------------
AL IMAN MEDICE CENTRE
Wannan wani kantin saida magungunane dake kawon maigari wannan waje suna saida ingantattun magunguna masu kyau kuma suna sayarwa ccikn sauki sannan suna bada magani ga masu cutar iska ko amusu rukiyya cikin sauki muna da malamai masuyin wannan aiki kamar malam Nuara/ Malam Salimwannan waje mallakar Dr kamal mohd Giginyu wanda ya kware gaya wajan bada magani kuzo ku jarraba(Email:kamalgiginyu@yahoo.comKAMSHI GENERAL ENTER PRISESKamshi general enter prises wajan saida turarene masu kamshi kamar yadda aka ambata ana kawo turaruka kala kala wanda ba ko ina ake samun suba saidai a kamshi ana hadawa mutum turare irin wanda yakeso kuma munada gwaji akwai alakoro kuma duk karshen wata muna Bonanza dan jin dadin al,umma wannan waje yana kan adreshi kamar haka N0:3 Ibrahim kallah R oad Giginyu (Saleem ibrahim kallah

SAMINU MINISTER REPAIR AND MANTENANCE
Muna gyaran kekuna kala daban daban komai tsufansa koko akawo sabo muyi sabis mu hada cikn farashi mai sauki munada in gantattun kayan aiki na gani na fada wannan waje yana kan titin lafiya road dafda kwanar sultan road kusa da odunma (Saminu minister)

IBRAHIM MAI GYARAN BOHOLE
Malam ibrahim yana gyaran rijiyar burtsatse koko hada sabuwa yana bada garanti acikin aikinsa babu hainci ba mina miuna aiki kamar a turai sai a naimi ibrahim a unguwar giginyu gidan hajiya yar'takayye (Ibrahim Iro)

WASA KWAKWALWA
Wasu mutanene su uku suna zaune su hira a bakin hanya sai sukaga wani mutum ya wuce da kaya akan mashin sai daya yace yanzu haka daga sabon gari yake sukace kwarai sai ko yace kunga yanzufa nasan iya yawan mutanen da suke kasuwar sabon gari,sai dayan yace ai kai baiwarka yar kadance nifa duk wanda na gani a kasu warnnan nasan sunansa,sai dayan yace to aiko duk na fiku baiwa domin kuwa ni duk nasan gidajensu, dan allah wa yafi kar anan.

TELA DA MAI GYARAN RADIO
Waiko tsakani tela da mai gyaran radio waye yafi rashi cika alwari


MU KYAKYATA
Wani barawone ya sato mota sai barayi suka tareshi sukace yabasu mukullin mota ya dauko yabasu yace amma karkubi ta wannan hanyar dana fito dan nima daukota nayi sai sukace a ai tundama abokin aikine abashi kawai yatafi ya iyo tafia kamar minti goma sai yansanda suka tareshi suna cewa kai ina takardun mota sai yace haba yallabai me kuke anan ga motar banki can ta fadi da kudi aciki dazafinsu sukace waca hanyace saiya nuna musu baya inda barayi suke sukahau mota suka tafi da sauri suna zuwa barayi suka biyosu suka sauka sukabar motar tasu barayin suka dauke.,

BABARBARE
Wani barbarene yazo kano daga maiduguri yanada dan tab'in hankali sai yazo wajan wasu mutane yayi musu sallama suka amsa ya zauna agefe lokacin sallar magriba yayi kowa yayi alola shidai bai motsaba,to an ganshi yayi shiga irinta manyan kaya ga alkaybba ga rawani sai mutane sukace bisimillah aramma ya shiga gaba yafara sallah yakaranta fatiha saiya fara jawo bakara mutane suna tsammani kadan zaikaranta mutumin naka kuwa karatu kawai yake wasu harsuka gaji suka fice daga jam,i bayan anyi sallama sai wani yace kai amma malam ansha karatu yace ai damma banyi alola bane da abin yafi haka.

BUZU
Wani buzune yasayo tsire yazo bakin bishiya ya zauna zai faraci ya baje takrda kawai sai shirwa ta sauko ta dauke ledar gaba taya ya tashi zaibita da gudu yaga tayi sama babu yadda zaiyi sai yace jeka na baka sadaka dan tsuntsu.BUZUWani buzune yazo wajnni wani malami yana gaya masa irin mafarkin da yayi yace ala gafarta malam nayi mafarki ina kan rakumi,malam yace mutuwace, yayi sauri yace saina fado,malam yace wahalace,yakumayin sauri yace saina makalkale,malam yace talaucine buzu yace to banni anan.

DAN GIYA
Wani dan giyane kullum idan ya shawo sai yazo wata majlissa ya tsaya yayta basu dariya rannan sai akayi mitin cewa wannan mutuminfa duk abinda yakeyi dan yaga ana yin dariyane amma yau idan yazo komezeyi kar ayi dariya anacikin haka sai kuwa gashi allah yakawoshi yana isowa sai fara abindariyar daya saba kowa yayi shiru dukta yadda yayi bawanda yayi dariya daya gaji saiya dage kafa daya ya tsaya kan yatsansa daya yace na shekara ahaka sai darira.

ZOMO DA ZABO
Zabone yana tsaye akofar gidansa sai ya hango zomo yaga kunnuwannan atsaye yanaso ya tsokani zomo yanjin kunya zomo da y'ay'ansa suna zuwa kusa da zabo sai yace a,a mutanan arziki kun nufo tananne zomo yagane wannan tsokanace daya kalli kan zabo yaga kora yace i wallahi aiko rannamma tanan muka wuce

AN KASHE DAN UWA MUSULMI

Babban Labarinmu
An yi wa dan uwa musulmi kisan gilla a Jaji

A ranar Juma’ar nan 14/12/1426 ne wasu gungun samari da suke kiran kansu da ’yan Salafiyya suka yi wa wani dan uwa mai suna Malam Musa Muhammad kisan gilla sanadiyyar dukan sa da fassakare a mukamukinsa da suka yi.
Yadda wannan al’amari mai ban al’ajabi da takaici dai ya faru, kamar yadda Malam Shu’aibu mai wakiltar ’yan uwa na yankin Jaji ya bayyana mana, shi ne, wasu ’yan Salafiyya ne guda biyu, Abdulkadir, wanda yake kani ne ga Hakimin Jaji, sai wani wai shi Sufyanu,suka zo gidansa kafin aukuwar wannan lamarin, suka ce masa ya shirya za su zo su yi wa’azi, za su zagi Imamu Khumaini da Malam Zakzaky (H) a ranar Juma’a 14/12/1426, su zartar da kisa gare shi.
Ganin haka ya sa saboda maslaha sai ’yan uwan suka je wajen Hakimin Jaji, suka yi masa bayanin komai da komai, ya kuma dauki alkawari ganin cewa hakan ba ta faru ba.
Amma duk da haka sai ga shi ’yan Salafiyar sun yi gangami daga wurare daban-daban a ranar Juma’a 14/12/1426 a wani masallacin Juma’a da ke kusa da bakin titi unguwar Fata a nan Jaji suna zage-zage da cin mutuncin bayin Allah.
Akwai wasu ’yan uwa hudu da aka tura su musamman domin su tsaya a gefe su ji irin hukuncin da za a yanke, isar su ke da wuya, kamar yadda Malam Mhammad Sani mai ruwan bara’a ya shaida mana, sai ’yan Salafiyar suka kama su da duka. “Wani dan Salafiya da ake kira Abubakar Auta, wanda kuma shi ne ya kashe Shahid Musa ya kama ni da kokawa har ya yi sanadiyar wannan ciwon nawa na kafa”
Shi kuma wani dan uwa mai suna Malam Ibrahim cewa ya yi, kanin Hakimin ne ya kama shi suka shigar da su masallaci suka gotar da shi a kafa, kuma suka sare shi a ka, sai kuma wani dan uwa mai suna Muhammad Musa da suka yi wa rauni a cikin kunnensa da kuma kansa sakamakon wani abu mai tsini da suka caka masa a cikin kunne.
Ana cikin haka ne sai ga Hakimi Abdurrashid ya shigo cikin masllacin, kuma a daidai wanan lokaci ’yan uwa da yawa sun ji labarin abubuwan da ke faruwa, saboda haka sai suka garzaya masallacin, inda suka kwaci ’yan uwan da ’yan Salafiyar suka yi garkuwa da su.
Bayan kwato ’yan uwan da aka yi, sai wasu ’yan uwa suka ce a biya su diyyar wadannan ’yan uwan nasu da aka raunata a lokacin suna magana ne da Hakimi da kuma wani SP na ’yan sanda wani mai suna D. Ladan.
Ana cikin haka ne sai ga Shahid Musa Mahmud ya zo ashe a daidai wannan lokacin akwai wani kawunsa da ’yan Salafiyan suka kama har sun raunata shi, sai ya ce ai lalle ya kamata a kwato shi. Ana cikin wannan zance ne fa sai wuri ya hargitse. Hakimi na wurin SP na ’yan sanda na wurin, amma ba su dauki matakin hanawa ba. a sanadiyyar haka ne wani dan Salafiya mai suna Abubakar Auta, wanda shi ne Kwamandan ’yan Salafiya na Jaji ya sa fassakare ya buge Shahid Musa Muhmud a mukamukinsa, wani kuma dan Salafiyar ya daga katuwar marmara ya buga masa a kirjinsa, wanda ya yi sanadiyyar shahadarsa nan take.
Zuwa wani dan lokaci ne sai aka turo ’yan sanda da sojoji masu yawan gaske aka rarraba su a wurare daban-daban saboda tsoron kada rikicin ya fantsama cikin gari.
Washe gari ne dai da safe aka yi wa Shahid Musa Mahmud salla a garinsu da ke Dandami a gundumar Birnin Yero, wanda Malam Abdulhamid Bello ya jagoranta. ’Yan uwa ne dai daga sassan daban-daban suka halarci jana’izar, wanda ya hada da Kaduna da Zariya. A cikin ’yan uwan da suka halarci wannan jana’izar da akwai Malam Mukhtar Sahabi da sauran ’yan uwa daga yankuna daban-daban.
A karshe dai Malam Abduhamid Bello ya isar da sakon Malam Zakzaky (H) na ta’aziyya ga ’yan uwa da iyalan Shahidin da kuma fatan Allah (T) ya karbe shi a matsayin Shahidi.
Shi dai Shahid Musa Mahmud Bafullatani ne haifaffen Kano a Karamar Hukumar Karaye, shekarunsa 37. Ya yi shahada yana da mata daya Zulaihatu da ’ya ’ya uku, Ibrahim mai shekaru biyar, Fatimah uku, Isma’il daya.
Wakilinmu ya tattauna a gurguje da Hakimi da SP na ’yan sanda wadanda suna wurin, wannan kisan gilla ya auku. Ga yadda hirar take:
ALMIZAN: Da yake ba yau ne irin wannan abin ya taba faruwa ba a wannan garin na Jaji, kuma ga shi su ’yan uwa sun sanar da kai tun kafin faruwar wannan abin, ko wane irin mataki kuka dauka a kai?
HAKIMI: Haka ne ai lalle mun dau matakai cewa ba wanda zai sake wa’azi a garin sai da izini.
ALMIZAN: An ce yallabai yana cikin masallacin da wannan al’amari ya faru shi da SP na ’yan sanda domin ’yan uwa sun je sun sanar da shi, kuma an ce a gabanku aka kashe Malam Musa, ko wane mataki ka dauka domin ganin haka bai faru ba?
HAKIMI: Lalle haka ne ina wurin, ina kuma kokarin hanawa. Amma sai da ya faru. Amma shi wanda ya yi kisan Abubakar Auta ne, shi na musamman ne, don mun riga mun dauki sunansa mun mika ga hukuma. Kuma yanzu na dawo daga Kaduna wajen mai martaba (Sarkin Zazzau) domin in sanar da shi. Na je Zariya aka ce min ya zo Kaduna, na bi shi Kaduna, ina zuwa na tarar har sun shiga wurin taron da ake yi a Kaduna. Amma in sun tashi zan je in sanar da shi.
ALMIZAN: Wadanne irin mataki ne ’yan sanda suka dauka kan faruwar wannan lamari.
SP D. LADAN: Farko dai mun dauki (statement) na wadanda aka ji wa rauni, su kuma sauran wadanda suka aikata wannan aiki mun dauki sunansu.”
A ta nasu bangaren kuma su ’yan Salafiyyar sun ari talaman kare sun bar garin ba wanda muka gani balle mu tattauna da shi.
Al’umma dai sai Allah wadai suke, kuma sun sa ido don ganin me hukuma za ta yi a kai ganin cewa wannan ba shi ne na farko ba, kuma ma gaban su hukumomin garin al’amarin ya faru.

KISAN MATAR RIMI

Babban Labarinmu
Rashin imani!
An gano wadanda suka yi wa matar Rimi kisan gilla kuwa?
Daga Ali Kakaki alikakaki2001@yahoo.com
A ranar Asabar da ta gabata ne al’ummar birnin Kano da ma kasa baki daya suka wayi gari da mummunan labarin kisan gillan da wasu ’yan ta’adda marasa imani da tausayi, wadanda ba a san ko su waye ba suka yi wa Hajiya Sa’adatu, matar tsohon Gwamnan Jihar Kano na Farko na farar hula, Alhaji Muhammad Abubakar Rimi, kisan gilla ta hanyar yi mata yankan rago.

Yadda abin ya faru, kamar yadda Halimatu Sadiyya, ’yar Yayan Rimi ta shaida mana, shi ne ita dai Hajiya Sa’adatu Abubakar Rimi bayan ta kwanta barci da misalin karfe 2:30 na dare aka je aka yi mata yankan rago har cikin dakin kwanan mijinta, tsohon Ministan sadarwa, Abubakar Rimi.
Sadiyya ta ce suna kallo tare da ita barci ya kwashe marigayiyar har aka gama kallon fim din, sannan ta farka ta tambaye ta yaya fim din ya karke, ta shaida mata, sannan suka je suka kwanta a dakinsu, “ita ma Hajiya ta je kakin Baba ta kwanta.”
Sadiyya ta kara da cewa bayan sun kwanta, ta fito shan ruwa, sai ta ga wani abu wanda ba ta taba gani ba, inda ta ce akwai wani fitila na lantarki wanda ba ta taba ganin an kashe ta ba wanda take kofar dakin Rimi, amma sai ta ga an kashe ta. “Yunda na ga haka jikina bai ba ni ba, sai na dauka Hajiya ce ta kashe. Sai na koma na kwanta. Da gari ya waye sai Ma’u (Asama’u) wacce ita ce ’yar autan marigayiyar ta zo tana tashi na, tana cewa Mama! Mama! Ta mutu. Muna isa sai muka samu Hajiya an kashe ta, an yanka mata wuya jini face-face, har ya fara bushewa,” in ji Sadiyya.
Maigidan marigayiyar, Alhaji Abubakar Rimi, ALMIZAN ta samu rahoton cewa a wannan rana ta Juma’a sai da ya yi sallar magriba a gidan Musa Gwadabe sannan ya kama hanyarsa ta tafiya Kaduna wajen taron tunawa da Sardauna. Bai kwana a Kano ba a gidansa na Kaduna ya kwana.
Ana ta kyautata zaton cewa makisan, Rimi suka je nema, ba su same shi ba suka kashe uwargidansa Sa’adatu.
ALMIZAN ta ji jama’a suna ta fadin albarkacin bakinsu kan lamarin, wasu su ce ’yan fashi ne, wasu kuma su ce abokan hamayyar Rimin ne na siyasa suka yi hankoron kawar da shi daga doron kasa.
Sai dai kuma Alhaji Hamisu Dan Wawu Fagge, makusancin Rimi, sannan kuma mutumin da Rimin ya yi ma waya daga Kaduna ya shaida masa cewa an kashe matarsa, wanda da shi da jami’an tsaro suka shiga suka samu gawar Sa’adatu, ya bayyana wa manema labarai cewa ba ’yan fashi bane, yana ganin abokan adawarsu ne kawai. In da ’yan fashi ne ai za su kwashi sarkokinta na gwal, amma ba a dauka ba, kashe ta kawai suka yi.
Rundunar ’yan sanda ta kasa ta saka ladan kudi Naira Miliyan biyar ga duk wanda ya tona asiri, aka gano wadanda suka yi kisan.
A ranar Litinin ne kuma Jami’an tsaro karkashin mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda na kasa, DIG Mista Olaban, mai binciken manyan laifuka, ya bayyana wa ’yan jarida cewa suna tsare da Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, tubabben Sarkin Dawaki mai Tuta, har sai an kammala bincike bisa zargin wai ko yana da hannun a ciki.
Kafin a kama Aminu Babba Jami’an tsaro na tsare da mutum goma sha uku a kan lamarin, wadanda suka hada da masu gadi da kuma wasu ’yan aikin gidan na Rimi.
Sai dai kuma abin da jama’a suka zura ido su gani shi ne gano hakikanin gaskiyar lamarin kisan gillar da aka yi wa Hajiya Sa’adatu, kar lamarin binciken ya bi shanun Sarki, kamar yadda na Isyaku Muhammad da Bola Ige da kuma Harry Marshal suka bi shanun Sarki, babu cikakken rahoton da ya fito a kan kisan da aka yi musu.

AN SACE WATA YARINYA

Babban Labarinmu
Daga zuwa amso kayan wanki:
Ta tsinci kanta a gidan yankan kai
Allah ya kubutar da wata yarinya da masu yankan kai suka sata suka kai ta daya daga cikin gidajen yankan kai da ke cikin garin Kaduna ranar Juma’ar nan da ta gabata.

Fatima Umar, da aka sace
Daga Aliyu Salah
Fatima Umar, 14, ta bayyana wa ALMIZAN cewa ta fito daga gida inda aka aike ta ta karbo kayan wanki; ba ta fi miti daya da fitowa ba, sai kawai ta hadu da wani mutum a wani lungu ta kauce masa domin ya wuce (da yake lungun mutane biyu ba sa wucewa a lokaci guda) kamar yadda aka saba, amma sai mutumin nan ya jefe ta da wani dan karamin dutse da ke hannunsa, daga nan sai ta tsinci kanta a gidan yankan kai. “Da na kauce masa, sai ya jefe ni da wani dutse, tun daga nan ban sake sanin inda nake ba sai kawai na gan ni a cikin gidan yankan kai.”
Fatima Umar ta ce, dakin da ta samu kanta a ciki, su 26 ne da suka hada da maza da mata, yara da manya, wadanda su ma da alama an sato su ne. Ciki kuwa har da wani Malaminsu da ya karantar da su a makarantar boko da kuma wasu yara kamar tagwaye cikin kayan salla, kowa ya yi zugum, wasu kuma suna ta kuka.
Ta ce, lokacin da wata mata ta shigo, sai ta lura su uku sun hada kansu suna ta addu’a da kuka kamar yadda sauran suke yi, “sai wannan matar ta ce wadannan yaran tsinannu ne a canza mana wajen zama.”
Fatima Umar, wacce daliba ce a Madrasatul Tas’hihul Iman da ke Badarawa Kaduna, ta bayyana cewa, a lokacin da suke sabon dakin da aka canza masu ne, daya daga cikin wadanda aka mai da su wannan dakin, wacce ta ce mata daga Zamfara take ta dawo hutun kirsimeti ne aka kama ta aka kai ta nan wajen, ta ba su Alkur’ani wanda ke cikin jakarta ta makaranta ta fara karanta masu.”
Yayin da take cikin wannan karatun ne, sai Allah ya nufi tashin wata wuta a wani bangare na cikin gidan, sai masu gadin su suka mai da hankalinsu ga wutar da ta tashi a cikin gidan, sai su kuma suka yi amfani da wannan damar suka fito daga dakin da aka kulle su suka gudu daga cikin gidan yankan kan. “Ana haka ne muka ga wata kofa sai muka cire sakatar kofar muka fito daga cikin gidan muka yi ta gudun tsirar da kanmu.”
Fatima Umar dai da alama ta jikkata sakamakon gudun famfalakin da suka yi don su tseratar da kansu. Ta ce, su ukun da aka canzawa daki ne suka kubuta daga wannan gidan. “Mun dade muna gudu sai muka tsaya a wani waje don ba mu san inda za mu yi ba. Daga nan sai muka ci gaba da gudu, daga bisani sai muka samu wasu gidaje. Sai na ga wani waje an rubuta Bamako Street. Daga nan kuma sai muka ci gaba da gudu. Da na juya baya sai na gan ni ni kadai. Na ci gaba da gudu har sai na kawo wajen wani mutum da yake sayar da su dabino da sauran kayayyaki a wajen.”
Lokacin da ta iso wajen sai ta fadi kasa ta kasa magana, ba ta iya tashi, sai mai wannan shagon da ke kan mahadar Raba/Wurno kusa da gidan rediyon KSMC ya ba ta ruwa, kafin daga bisani ya tambaye ta abin da yake faruwa. Ita kuma ta bayyana masa duk halin da take ciki da kuma taimakon da take bukata daga wajensa.
Wasu ’yan agaji ne suka kai ta gida bayan sun tarar da ita a wajen wannan mutumin hajaran-majaran, mutane suna ta kallon ta sakamakon yanayin da suka ga ta samu kanta a ciki.
Fatima Umar ta bayyana mana cewa, kodayake ta iya gane yanayin gidan, amma ba za ta iya gane gidan da aka kai ta ba. Kuma ta ce ba za ta iya tantance mutumin da ya sace ta ba, “domin ban sake ganin sa ba tunda ya jefe ni da dutsen.” Ta ce gidan babban gida ne, sai dai ba su ba ta komai ta ci ba.
Daya daga cikin yaran da suka tsira a wannan gudun da suka yi, ta bayyana wa Fatima cewa a ranar da aka kawo ta an kawo mutane bakwai gidan. Kuma suna cikin gidan sun ga an dauki wasu mutane biyu daga dakinsu aka fitar da su aka kai su wani dakin na daban, wanda daga bisani suka fahimci cewa an kai su mayanka ne an yanka su.
Da yake yi wa ALMIZAN bayani game wannan abin bakin cikin da ya faru da su, Injiniya Ibrahim Adamu Hadeja, ya bayyana matukar jin dadinsa da samun sa’ar da suka yi Fatima ta dawo gida lafiya ba tare da wani abu ya faru da ita ba. “Dole ne na gode wa Allah, domin wannan abin ba tun yau ba, muna jin labarinsa sai ga shi ya zo gare mu.”
Ya nuna takaicinsa game da yadda hukumomi suke nuna halin shakulatin bangaro game da hukunta wadanda ake aikata wannan mummunan laifi na satar mutane suna tsaface-tsaface da su don neman duniya.
Ya tabbatar da cewa satar mutane a ’yan kwanakin nan ya yi tsanani, ya zafafa, “da dai abubuwan sun yi sauki, amma kuma yanzu ya dawo. Ya kamata mutane su nema wa kansu magani kada su dogara da hukuma domin su ba wannan ne ya dame su ba. Da abin su yake shafa da yanzu sun yi maganin wannan matsalar, amma da yake abin mu (talakawa) yake shafa shi ya sa abin bai dame su ba. Da muna da shugabanni masu adalci da tsoron Allah da wadannan abubuwan ba za su faru ba.”
Don haka sai Injiniya Ibrahim Adam ya yi kira ga iyaye da su rinka kaffa-kaffa da kuma sa ido sosai a kan ’ya’yansu, su daina barin su suna yawo sakaka ba tare da kula da su ba. “Idan gwamnati ba za ta iya yin wani abu ba, gaskiya tilas ne mutane su dauki matakin da za su kare kansu, su kare rayukansu da dukiyarsu,” ya jaddada.

TARIHIN HAUSA

Tarihin Hausawa

Kabilar Hausa dai,kabilace dake zaune a arewa maso yammacin taraiyyar Nijeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Kabilace mai dimbin al'umma, amma kuma a al'adance mai mutukar hadaka, akalla akwai sama da mutane miliyan hamsin da harshen yake asali gare su. A tarihance kabilar Hausawa na tattare a salasalar birane.Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai,Borno da kuma Fulani. A wasu lokutan Hausawa sun sami gagarimin ikon, mulki da hadaka ta kau da baki'yan neman ruwa da tsaki,da kuma neman angizon a cikinta da kuma harkallar bayi. A farko-farkon shekaru na 1900's, a sa'adda kabilar Hausa ke yinkurin kawar da mulkin angizo na fulani,sai turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mamaye arewancin Nijeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida,a bisa karkashen mulkin birtaniya,'yan mulkin mallaka sai suka marawa fulani baya na cigaba da manufofin angizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin kamin gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne yayi kane-kane a arewacin Nijeriya. Wannan hadakar gamin kambiza, an farota ne tun asali a matsayin fulani su dare madafun ikon a tsararren tsarin siyasar arewa.Akasarin masu mulki na fulani sun kasance yanzu, a al'adance hausawa gwamitse
Ko da yake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma ya zuwan addinin islama da kuma karbansa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bambam.Ginshikokin al'adun hausawa na da mutukar zaranta, kwarewa da sanaiya fiye da sauran al'ummar dake kewayenta. Sha'anin noma ita ce babbar sana'ar hausawa inda hausawa ke ma sana'ar noma kirari da cewa, na doke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai yatarar, akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima watau harkar fatu, rini, saka da kira, fannonin dake mutukar samun cigaba a harkokin sana'o'in hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin yau da kullum, tare da masu mulki da masana. Harshen Hausa shi ne mafi girma da kuma mafi sanai'yar harshe a nahiyar Afirka, harshen hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci kana kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa al'adar cudeni-na cudeka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a da ba hausawa bane a nahiyar Afirka.
Bugu da kari, akwai cincirindon al'ummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacinta da kuma yankunan cinikayyar al'ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar ta zuwa aikin hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun ajami da aka buga tun kafin zuwan turawa yan' mulkin mallaka na birtaniyya. Har ila yau, kuma wani tsarin rubutu a ajame da aka kirkiro tun kafin zuwan turawa, da ba kasafai ake amfani da shi ba yanzu.

LABARI

wannan filina jafar giginyu zai dinga kawo muku wasu mushimman labarai da dimi diminsu saboda haka yaka mata mai karatu yakara kwazo ga wannan fili damun samun wasu kyaututtuka akoda yaushe zaku iya samunmu koda cikn dare bama katsewa haka nan bada jima waba wannan fili zai sakawa masu karatu muhawwara dancin mabura da kekuna allah nyabada sa,a amin